Top Songs By Umar M Shareef
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Songwriter
Lyrics
Bude cikin zuciya ki jefa ni
In na shige sam kar ki fidda ni
Bude cikin zuciya ka jefa ni
In na shige sam kar ka fidda ni
Dan mazari a kira gwanin rawa
In ya fito tilas a yo kalla
'Yar makaranta na fi so kunga
Bani shiri da diyar dake talla
Fidda gwanin ki kice ba gani ba
Je a gari kiyo shela
Nine na zama zabin ki
Daurin auren mu nayi dauki
Taron auren mu za'ayi bikin
Da ba a taba yi dangin mu
Na guji samarin zamani sun sanya budurwa tayi kwalla
Mai kwadayin sabon zani itace gayu ke yiwa illa
Nayi addu'an samun miji nagari kullum in nayi sallah
Dakai ya hadani a duniya
Rayuwar mu muyita mu sha miya
Nayi fata ko a lahira mu zamo tare a cikin aljannar mu
Taro da kwabo in har na samu ke zan ba ajiya
Domin yin amfani gare mu kai har ma da iya
Albarkar sa tasa ki dube mu yau mun zarce jiya
In mun bisu cikin lamarin mu muyo nasara
Hannu kyauta shike samu in har ya tara
Mudai sai fa mu kara godewa ba abinda yake damun mu
Rikita-rikita nai alkawari
Bazan sanya ka kuka ba
Kwarin gwiwa na karama
Bazan sa kayi rauni ba
In mun samu mu gode rashi ba zai sa muji komai ba
Allah shine ya bamu
In yaso baya bamu
Sai yanda kaso kake yi alkhairi Allah ya sada mu
Bude cikin zuciya ki jefa ni
In na shige sam kar ki fidda ni
Bude cikin zuciya ka jefa ni
In na shige sam kar ka fidda ni
Lyrics powered by www.musixmatch.com