Lyrics

Bazan rayu in babu ke ba (dan'uwa na) Kin zama bangare na jiki na yar'uwa ta Bazan rayu in babu kai ba (yar'uwa ta) Ka zama bangare na jiki na dan'uwa na Samun kwanciyar hankali na In same ki mata guri na Nasan zuciya bata kuna Idan kin ka zam mallaki na Dadi za ya zauna a raina, "Amarya" In ce miki ke ko kice min "Ango na" Dan'uwa na Yar'uwa ta Ranar ce nake jira tazo min Farin ciki a nunnuna min Kayan kitchen aunty ta sai min Abinci babu mai girka min Sunana ka canza ka ce min "Amarya" Ba ko shakka kai za nace wa "Ango na" Yar'uwa ta Dan'uwa na Nine naki ko'ina je ki fada Kowa yasan nice taka na jaddada Kece zanwa waka in naji kida Za nayi amshi kalmomin so zanta fada Murna ce tasa zana budo wushirya Niko inyi far-far da kwayoyin ido na Bazan rayu in babu ke ba (dan'uwa na) Kin zama bangare na jiki na yar'uwa ta Bazan rayu in babu kai ba (yar'uwa ta) Ka zama bangare na jiki na dan'uwa na Kamanni na da naki gun hali daya Shi ya sanya nake bidar mu zamo tsintsiya Kalamai na wa ke nake wa ke daya Na cinye, indai zani sa ki cikin dariya Burina a so ya cika masoya Idan da rai watarana kina gida na Kaine masoyi na farko In babu kai gani fanko Kai zana dama wa koko Ka sha da dadi a koko Idan na shige ban fitowa ni amarya In zauna da kai ba rabewa miji na Bazan rayu in babu ke ba (dan'uwa na) Kin zama bangare na jiki na yar'uwa ta Bazan rayu in babu kai ba (yar'uwa ta) Ka zama bangare na jiki na dan'uwa na
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out