Lyrics

Share hawayenki, amarya share hawayenki Miya ya dameki? Amarya wai miya ya dameki? Yau ake daura aurenki Ranar farinciki gareki Yau dake da 'yan uwanki Ango ya biya sadaki Saura a kaiki daki Je ki gaida iyayenki wanda su suka haifeki Masu tarbiya gareki A yanzu ke dubanki Farinciki sun baki Basu so suga kukanki Gashi yau ranar bikinki sun ga muna susuronaki Ki biyayya gurin ango Tunda yanzu shine jigo A gareki ya zam ango ma'ana mai kwarar daki Kinyi aure ibada Kunne ido ki kauda Kinji-kinji duk ki zubda zancen masu son su kulla yaki Ango amarya nai maka barka Kyakykyayawa ce amarya hakika A gida na tarbiya aka dauka Kwalliya gurinta sai son barka Lokaci yasa rawar dana taka Auren Allah yasa albarka Farinciki kuke ciki Maza da mata sun zo Mai bakinciki-bakinciki Muko bishi da kanzo Ranar biki yau ake biki Maza da mata sun zo Mata kuban guda Muyi rawa muyi rawa muyi rawa Har wani kamshi ma tashi yake Naga kawaye har juyi suke Abokai su ma sai taku suke Iyaye sai sa albarka suke M. Shareef mai waka Yanzu ma muka fara Kowa yazo ya taka Dan haka nan muka tsara Nai haka nai haka Kuma kuyi haka kuyi haka Mata kuzo da girgiza Mazaje sai ku a gaza Amarya zo ki rangaza Ango kizo Ki ingiza
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out