Lyrics

Eh komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Eh da sunan Allah arahimu sarki mai kyauta Rabbi zanyi salati gun rasulu daha baban Binta اللَّهُمَّ صلّ على مُحَمِّد mai tsabta وعلى آل da sahabuna masu yin bauta Rabbi na kawo karan bayin ka masu bari kuma ban fada ba Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Allah yayai mini baiwa Dole ne Zango nai godewa Dattawa suna kauna ta Maza da mata suna ta yabawa Matasa suna kauna ta Maza da mata suna tafawa Yan yara maza da mata In sun ga Zango suna darawa Amma makiya sun dage Bazasu bar Zango ya huta ba Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Eh in kun tina chan baya yan uba sunata cewa arne ne ni Da na fara waka sun kace Zango ai dan iska ne ni Album din bahaushiya shi ya kai ga gomnati ta daure ni Bayan na fito daga kurkuku taska ta kuma babu anini Sai nayi koyin manzo na Nai hijira zuwa garin Kaduna Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Zango nayo kokawa Wani lokaci kuma nai darawa Aka daina saka ni a fim Yan uba suna tai min darawa Suka ce ta kare min Zango yanzu babu tudun tafawa In naje gun umma ta Gabanta zana fadi ina kokawa Sai tace baba, daina kuka rabbi yana nan Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba A gari na Kaduna, kaddara ban iya kaucewa ba Ban san hawa ba ban san sauka ba Sai masifa yayai saukowa Daga chan gari na Sokkoto yan sanda sukayo taho wa Wai nayi waka na zagi Wamako shine suka taho chafkewa Rana zafi inuwa zafi dole nayo boyewa Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Zango sai na hau mota na gudu gidana ban zauna ba Aka kama min yan uwana su hudu babu dalili duba Eh Hafsa da Hamza, Sa'idu, Deeni kuka suke kuyi duba Daga nan aka je kotu sai prison aka kai su ku duba Toh kunji sharrin mahasada Su suka kula ban aikata ba Eh me kake son cewa ne ai Zango yan uba fa basa kyle ka Mun san labarin Sokkoto harda wanda aka so kashe ka Duk koshen mai koshe, wallahi Zango muna bayan ka Mu masoyan ka munji wai, kai wa Nafisa ciki ba shakka Warware zance mu gane komai Dan zuciyar mu tabar yin shakka Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba Toh me ka hango Zango? Daukaka da dadi wuya duba Nafisa Abdullahi lakani nata sai wata rana Masoyiyace agareni wanda kuka shaida tana kaunana Wata rana fagen yin aiki sai ga waya fa anata kirana Wai ana shari'a a Kanon dabo kotu gashi kana kai rana Har Kaduna ana yadawa duk dan a bata min sunana Wasu nacewa sun gan ni a kotu tana kara na Kaji aikin mahasada Ko kuce dani makiyana Kazafin su da duk sharrin su Duk gadon baina suka kwana Eh lalai kaji yan uba Masu son su gano baya Wanda duk ya riga ka a bacci Dole zai tashe ka a kwana Eh kayi gaskiya Rabbi ni na rika jigona Eh kaji zancen banza Sai ku dau hakuri mabiya na Makiya sai ku karo azama Baku iya ganin karshe na Masoya nan zan bar ku Rabbana yayo sakawa Komai daga Allah ne Mai daukaka bazai wuce sharri ba A ciki na sana'ar ka? Yan uba baza fa au kyale ba Wai menene Zango? Rayuwa cikin ta na duduba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out