Lyrics

Abinda rabbi yayi mutum bayi hanawa Amarya da ango sakon ku zanyi issar wa Ranar bikin aure ne, da team muka zo wa Mun amsa gayyata, wakar zan farawa A mar matsa mun bude filin taro Hamisu Breaker waka nazo taro Karku bani jawabin bayan taro Bikin aure mu ake bida a gaba Dan idan ba nama, miyar baza tayi ba Ke amarya taso a sannu tataka Kin samo miji wanda gunki babu tamka Shine zaya rike ki, baki yin kuka Kaima ango yau rabonka ka dauka Agunka muna kara furta sam barka Kamar yau ne za'a ce dakai kaka Ka amsa, jamma'a su dinga gaida ka Su dinga gaida ka Su dinga gaida ka Su dinga gaida ka (hayya kai) Haka zancen zan nutso, aure ya zamto sunna ne Ke amarya ga ango kiyi ladabi hakan din riba ne A gidan aure, nutsuwa ake karki bari daraja ta zube Soyayya yanzu zakiyi, da wasa farin girki ne Kinga ki chan-chada zo juya a gaban angonki In kinso kiyi mai rawa, haka bazai zamto ila ba Soyayya sa'a take, so mai sonka bazaka rasa ba So in yakai so, har yanayinku baza'a rabe ba Sabo kesa shakuwa, ya za'a yi bazan furta ba Dani da masoya, alkawari ne wanan babba Ke idan magana kike to daga murya ban ji ki ba Wai kunji tace in gaya muku soyayya zatai farawa Ita wanan agun nan tace kar in tonawa To nayi shuru haka nan gaba ai zakuyi ganewa So baya buya babu musu, kuyi duban ango Dole kanwar naki wanan taken soyayya ne So ya ratsa mu, yana a jikin mu halitta ne Zaman so a zuci kamar fitila bisa alkuki ne Ya wuce haka ma, na fadi misali ne Sanadin sa ake aure ayi zaunawa Nan zana karkare yan uwa Hamisu Breaker ne sunana Mai baituka na so har kauna Masoya rabbi yabar kauna Masoya rabbi yabar kauna Masoya rabbi yabar kauna
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out