Lyrics

Musax beat Da kin sanar dani nasani Da zuciyarki tazama tawa Amma a yanzu duk korafinki Baya biyan bukatar nufi Duk sanda so yaso fa'ida Kushen shi ai akwai tambaya In kin sanar dani nasani Da gunki zan matso in tsaya Nai sahiba guda kan idonki Ya zan nasota in kin taya Yau zuciyar ki ni tai riko Ni tawa inta tai zan raka ta Eh karki fishi dani mun dade Amma abotaka ce muke In zanaso amun rakiya Duk inda zani bina kike Kallon kawa nake yi miki Ashe a zuci sona kike Ga tawa wace nai wa gini A zuciyarmu ma tajike Yau sai nabarta danke kawai Na dau hakkin ta ai na bata Kin kuskure gurin anbatar So tunda baida ranar bari In ni kike bukatar riko Toh sai ki sake sabon shiri Na bada zuciya jiko Ranshinta kar ya koma baki Ban furta so ba ke kin sani Kema a yau kike ambata Ga wace nai wa karkon gini Na barta don na amsa miki Nasan abotaka ce muke Ba so bare na boye miki Kin boye naki dan dai kawai Kallo garemu ba shamaki Ga wace mun riga mun dade Nabi ki mai ko zan ce mata? Ke kinji yadda so dai yake Baya barin mutum lafiya Munyo ginin da kowa yake Fatan mu karasa lafiya Ya zaki zo ki rushe mana Amsar ki bani nai tambaya Kiyi hakuri idan kuskure Ni naki ne abun ambata Kiyi hakuri mu zauna kawai Muyi zumuntaka tai mana Nasan akwai jadali a so In ka bida ace an hana Kin aje naki har zuciya Takasama ta dau dangana Na tausaya rai zuciya Da kika baiwa ni adana Da kika bani yarda a yanzu Gareni babu gurbin aje ta Musax mix
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out