Lyrics

(Nexx) La-la-la, la'ila (yeah ah gat you) La'ila, la'ila Jama'a bacci fah ya fara kama driver Ya rage kowa yayi ta kan shi Burkin motan nan ma ya tsinke ku duba Jagaba ayi reverse Notin tayar motan mu fah ya kwance Jagaba ayi reverse (kai!) Wuta ta kama a bangaren tanki Jaba ayi reverse Don girman Allah motan nan tayi reverse (tayi reverse) Jagaba ayi reverse Mu gidan bikin da zaka kaimu ma bamu da pass Mu dai kawai ayi reverse Assalam Nazo daga lingeria ne Kasar da kowa na karba kauye-biranai Wahala, ba babba babu jinjiraye Inda mai mulki ke jin zai dauwama a duniya ne A kwana diru biyun bola An samu nasarar kara ma mai farashi Gwamnatin baya ta tara wa kasa bashi Biyan wannan bashin Baba Tinubun mu yake kishi An kusa kawo karshen zirga-zirga Za'a daidai ta kan yar gata da kuyanga Ubar kasan dai yace bamu kara gwanda Tun da in angama da man fetur za'a taɓa gona Dollar na kara bankarewa Muna burge America Kudu-Arewa Maciya amanar kasa ana rike wa Yanzu ma adashen ya fara mu dai muna zuba wa Tsaro ya samu hankalin kowa ya kwanta Ilimi kyauta a kowacce makaranta Kumatun mu subul-subul hannu na kanta Kuma ana rage fasinjojin motar makabarta Yaro Allah ma albarka Na rage ma murtala guda a kuɗin ka Nace Allah ma albarka Na rage ma murtala guda a kuɗin ka Da farko ni na kyautata ma zato Har wanda basu zabe ka ba sun kyautata zato Duba da irin tsarukan da ka fito Ammah wahalar tayi yawa daga Lagos har Sokoto Shikenan mu kullum haka mu zamu rayu? Muna da iyaye ku ringa maida mu marayu Ina fah gani a harkar nan da sake Al'umma fafutika muke da inda zamu rayu Kasar da arziki kuna gadar mana talauci Ba fah batun NEPA muke ba Babu titi mai kyau, tsaro idan ka duba Al'umma fafutika muke da yands zamu rayu Masu kiba sabewa Zirga-zirga harkan na kara rikicewa Tattalin arzikin mu ma yana kara rubewa Kuma ku kuka ce a baku harkan kuna iyawa Tura ta fara kai mu bango Lokaci bai tsayawa don bacin agogo Ba fah ca mukai ba ku ce mana ungo Ammah ko kadan bakwa hango abinda muka hango Wallahi muna ji a jikin mu Ko sau daya ne dom Allah aji kukan mu Jagaba ayi reverse Don girman Allah motan nan tayi reverse Hanyar da kuka bi damu bata da kyau Wasu sun wuce garin jibi muko har yanzu a yau
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out