Lyrics

Eh ana bugan ganga mai tashi Wadansu na doko harsashi Maza yanayi ya sauya Ehh Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya A rayuwa ta bani amintarwa da abin tsoro ne Mayaudari a cikin 'kauna ku gujeshi domin dodo ne Me tauye hakki shi yakamata muwa tofin Allah tsine Mukurkusa yau bashida damar yasha inuwa ta giginya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Eh ina kwatacen sonka kamar wata tsokance ajikina In akzo taro tauraro na kai 'daya zan nuna Ruwan ido ai bashida amfani mai yinsa ya daina Salon kidanka yabar rinjayarka koma kaji murya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Eh wanda yake kan dutse bai tsoron ayi wasan jifa Bakin jinini in yayi yawa kesa a kiraka da karfa Rashinna gaskiya ko a ruwa sam baya hana maka zufa Al-'kawari kaya ne mai nauyi gun wanda ya karya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya 'Kafa ta yaro in tayi 'kwari dole ya nemi ta ware Ya debi kasko keda su kwarkwasa ajikin su su tare Kai hankalin da abinda nike nuna maka kadda ka 'kware Dani dakai muzamo wasu taurari a cikin alkarya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Eh yanada kyau a cikin tafiyarmu mu dinga kuka da alaka Masan kare domin a jiya ya cijeni da fika Idan kakai bango a wajen kwazo kasamu hazaka Allah hadamu da wanda muke 'kauna ka raba mu da kunya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Eh asamu kyakkyawan 'karshe azama na masoya riba Saboda so zan shawarce mu nesa mu zauna turba Har abada mu rike junan mu mu 'kyale batun mai giba An walkiya a duhu yau ta haska mun farke laya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Eh ana bugan ganga mai tashi Wadansu na doko harsashi Maza yanayi ya sauya Ehh Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya Ganga ake doka mai tashi Fage na daga sai mai mashi Maza yanayi ya sauya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out