Lyrics

Na fahimta idan muna tare Lokaci yafi sauri Ai idan mun rabo Ina rayuwa cikin tari-tari Ban fahimtar ku wani zance Sai an yi mini kwari-kwari Ke kadai ce kika zuwar min Cikin tinanin mafari Kaddara ta dafare ni A sanki fili da sirri Yau idan kinka bar ni Ni zanayo kiran ajalina (Beat Alix production) Zuciyata na baki Domin kina da babban masauki Nayi niyar auren ki Ko zana badda duk yan kudina (Zuciyata) (Ke kadai ce) So farar damisa A chan nisa nada dadi na kallo Tunda dukan matsin shi Nan zaya sauya sunanka dolo Dukanin hakurinka sai ya kure ka Kazam mai hakilo Gashi tafin hanu Baya kare rana inda bulo So ruwan damina Ba mai iya tare shi In har ya balo Lokaci dai yake shiga Gun fitar sa sai anji kuna Ah-hh-hh-ah-ah-ah Ko ina nake Ko a mene nake zuciya bata tsira Naga karyar gudu a daji Kare idan yaga kura Zuciya ta rufe da so Na duhu bai gane harara Babu zahiri idan dai kare Ya mace saura Na rika na kware a so Yanzu banda sauran dabara Har idan zana ganki Toh zana mance duk matsayina Ah-hh-hh-ah-ah-ah Tabbatar min da so cikin zuciyar ki Ko naji sauki Ya ki kashe min wutar dake ruruwa Tabar yin hayaki Sauya min ruwan madaci Kiban zuma tafi zaki Takaita nisan mu banda burin Ki dauke halina naki Kadaita taraiyar mu zaman lafiya So yafi yaki Dan ni ko dan gidan ku Kishi nake idan zaku gana Na fahimta idan muna tare Lokaci yafi sauri Ai idan mun rabo Ina rayuwa cikin tari-tari Ban fahimtar ku wani zance Sai an yi mini kwari-kwari Ke kadai ce kika zuwar min Cikin tinanin mafari Kaddara ta dafare ni A sanki fili da sirri Yau idan kinka bar ni Ni zanayo kiran ajalina
Writer(s): Isah Ayagi Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out