Lyrics

Da soyayyata nazo (C one producer) Eh da soyayyata nazo Da so zan koma gida Da alkhairi na nazo Nayi rashin ka ina ruwa Oh, oh, oh Eh rigar so na sako Da so zan koma gida Furannin so na riko Nai rashin ka ina ruwa Tabaron so zan sako Da so zan koma gida A yau sonki nake dako ki sauke ni muje gida Da so zan koma gidana Eh rawa babu ya mazari Da so zan koma gida Cikin rai nayi ma guri Nayi rashin ki ina ruwa Ganinka nake marmari Da so zan koma gida Na zo gunka da hanzari ka tarbeni muje gida Da so zan koma gidana Eh cikar hula ko kuwa Da so zan koma gida Ni dake munyo shakuwa Nayi rashinka ina ruwa Rayuwa zamuyi sabuwa Da so zan koma gida Dake bama rabuwa a turmin tsakiyar gida Eh maza duka basu kai kaba Da so zan koma gida Da kai bana fargaba Nayi rashin ki ina ruwa In baka ba zan moruba Da so zan koma gida Kai zakai mun garkuwa waje ko a cikin gida Eh dama so ruwan zuma ne Wani sa'in ruwan guba ne Na kekkewaya birane So mai aji-aji ne wuce duka mai gida Da soyayyata nazo Da so zan koma gida Da alkhairi na nazo Nayi rashin ka ina ruwa Oh, oh, oh Mixed Golden Voice Da so zan koma gida na
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out